Cikar MƊD Shekara 80: Nasarorinmu sun ƙara mana ƙaimi da kyakkyawar makoma a nan gaba
Shekara 80 da suka gabata a makamanciyar wannan rana, an rattaba hannu kan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya (MƊD) a San Francisco, inda aka sauya tsari na yaki da duniya ta fuskanta shekaru da dama zuwa samar da kyakkyawar makoma.
Tsawon shekaru 80, MƊD ta tsaya a matsayin mai bayyana fatanmu na hadin gwiwar ƙasa da ƙasa, mai bayyana ma’anar burinmu na kawo ƙarshen “cutarwa a yaƙi.” A cikin wannan duniyar da ke cike da son zuciya, wannan muhimmin mataki ne da ya dace a ɗauka.
MƊD ta kasance ƙungiya ɗaya tilo da bata da tamka, kuma ita kadai ce ta dawwama. Wannan tsayin daka yana da ban mamaki idan muka yi la’akari da yanayin kafuwarta.
Babu wata ƙungiya da za a ce ba ta da aibi. Amma domin a bayyana ƙoƙarin Sakatare-Janar dinta na biyu, Daga Hammarskjöld: An kafa MƊD ba don ɗaukaka ɗan’Adam ba sai don cetonmu daga mawuyacin hali, kuma ba za ta gaza a kan wannan manufa ba.
Muna sane da wuraren da ake yaƙi masu taɓa zuciya: Gaza, Sudan, Ukraine da sauran wurare. Rikicin baya-bayan nan tsakanin Iran da Isra’ila, wani abin tunatarwa ne ga raunin zaman lafiya musamman a yankin Gabas ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula.
Duk da haka, a cikin wannan tashin hankali, mun yi nasarar dakile yakin duniya na uku. A wannan zamani na nukiliya, wannan nasara ce da ba za mu taba ɗauka da wasa ba. Ita ce wacce ta kamata mu kiyaye da ƙarfin ƙoƙarinmu.
A cikin shekaru 80 da suka gabata, yawancin ci gaban dan’Adam shi ma yana da tasiri a MƊD kai tsaye. Yi la’akari da nasarar da aka samu ta ci gaban karni, wanda ƙasashe mambobi 189 suka karɓa a cikin ƙasashe 2000 da ƙari.
Fiye da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa 20 ne suka ba duniya taswirar hanya ɗaya domin ɗaukar mataki.
KU KUMA KARANTA: MƊD ta saki dala miliyan 5 a cikin shirye-shiryen ambaliyar ruwa, amsa gaggawa a Najeriya
A 2015, idan aka kwatanta da 1990, matsanancin talauci ya ragu sama da rabi. Mutuwar yara ta ragu da kusan kashi 50 cikin ɗari. Kuma miliyoyin yara musamman ‘yan matan da ake dannewa haƙƙi sun shiga makaranta a karon farko.
Akwai wani muhimmin labarin ci gaba, wanda ba a mantawa da shi, shi ne wargaza daula. Shekaru 80 da suka gabata, mulkin mallaka ya yi shuhura a duniya. A yau, fiye da 80 da aka yi musu mulkin mallaka a faɗin Asiya, Afirka, Caribbean, da Pacific sun sami ‘yancin kai kuma sun shiga MƊD. Wannan canji da wannan Ƙungiya ta goyi baya kuma ta halalta shi ya sake fasalin tsarin duniya.
Shiga Tsakani domin samar da ci gaba
Duniya ta canza sosai tun daga 1945. A yau, jungiyar na fuskantar matsalar ƙarancin kuɗi. Duk da alƙawarin da aka yi na 2030 don samar da ci gaba mai ɗorawa, ci gaban kuma bai daidaita ba. Daidaiton jinsi ya ƙubuce mana. Alƙawarin da muka yi na takaita hauhawar ɗumamar duniya da kare duniyarmu ya karanta.
Waɗannan koma baya ba sun haifar da raguwar buri amma su ne manyan kudurorinmu. Majalisar Ɗinkin Duniya na nuna kimarta a lokutan rikici.
Waɗanda suka kafa ta sun shaida dan’Adam a matsayin mafi barna kuma ba su yanke kauna ba, saboda karfin hali. Dole ne mu zayyana wadannan nasarori.
Yayin da muke bikin wannan zagayowa, dole ne mu sake farfaɗo da ƙiran haɗin kai da aka yi daga San Francisco shekaru 80 da suka gabata.
Mun gina tsarin duniya farat ɗaya, domin rushe tsarin yaƙi, mun yi hakan ne da hangen nesa cikin gaggawa. Yanzu kuma, mun sami kanmu a lokacin sakamako. Haɗarin yana da yawa. Haka zalika kuma karfinmu na yin aiki na da yawa.