Boko Haram a Yobe sun kashe mutane da dama da ƙona gidaje
Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun hallaka mutane da dama, suka ƙona gidaje da kantuna tare da wawushe kayayyaki a ƙauyen Mafa da ke ƙaramar hukumar Tarmuwa ta Jihar Yobe.
Mayaƙa sama da 50 ɗauke da muggan makamai a kan babura ne suka far wa ƙauyen a yammacin ranar Lahadi.
Jami’in hulɗa da Jama’a na ’Yan Sanda a Jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ne ya tabbatar da harin a Damaturu a safiyar Litinin.
DSP Dungus ya ce shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa “Zuwa yanzu ba mu tantance adadi rayukan da aka rasa ba, a harin da aka kai da misalin karfe 4 na ranar Lahadi.
“Wani daga ƙauyen Mafa ne ya kai rahoton harin ne a Babban Ofishin ’Yan Sanda na ƙaramar hukumar Tarmuwa.
KU KUMA KARANTA: Mun kashe ’yan boko haram 5, 44 sun miƙa wuya – Sojojin Najeriya
“Mayaƙan, ɗauke da manyan makamai har da RPG sun far wa gundumar Mafa, suka ƙona gidaje da kantuna.
“Sun kuma kashe mutane da dama, amma ba a kai ga tantance adadinsu ba,” in ji DSP Dungus.
Ya ƙara da cewa maharan sun kuma jefar da wasu takardu masu ɗauke da rubutun Larabci.