Boka ya kashe surukarsa bayan ta gano yana lalata da ƙanwar matarsa ​​

0
558

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun kama wani boko shekara 38 bisa laifin kashe surukarsa.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Legas Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Hundeyin, wanda bai bayyana sunayen wadanda ke da hannu a lamarin ba, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa; “a wani wuri a Akodo, wannan mutum mai shekaru 38 ya kashe surukarsa, sai kawai ya gano wani ya gan shi yana aikata laifin, nan da nan cikin sauri ya kashe mutumin da ya gan shi.

“Wanda ake zargin yana tsare kuma bincike na farko ya nuna cewa ya kashe surukar tasa ne saboda ta gano cewa yana lalata da ƙanwar matarsa ​​‘yar shekara 14 kuma ta sha alwashin kai ƙararsa” inji shi.

Yace an tura wanda ake zargin zuwa sashen binciken manyyan laifuka na SCID domin zurfafa bincike da gurfanar da shi a kotu.

Leave a Reply