Birtaniya Za Ta Bai Wa Ukraine Tallafin Makamai Da Kudade

0
285

Daga Wakilinmu

Birtaniya za ta bai wa Ukraine taimakon motocin yaki na igwa har 120 da makamai masu tarwatsa jiragen ruwa da na harbo jiragen sama baya ga tallafin kudi.

Fadar gwamnatin Birtaniyar ce, Downing Street ta sanar da haka bayan wata tattaunawa a ziyarar bazata da Boris Jonson ya kai wa Shugaban Ukraine Volodymr Zelensky a Kyiv.

Firaministan ya gana da Shugaba Zelensky, a abin da fadar gwamnatin Birtaniyar ta kira nuna goyon baya ga Ukraine.

Daman tun kafin yanzu Firaministan ya zaku ya kai wannan ziyara, amma ya tsaya yana jiran yanayin tsaro ya inganta a babban birnin, bayan janyewar dakarun Rasha daga yankin.

A yayin wannan ziyara wadda ta kasance ta baya-bayan nan ta wani shugaban kasar yamma, fadar gwamnatin Birtaniyar ta ce, kasar za ta tabbatar da bai wa Ukraine karin tallafin dala miliyan 500 ta hanyar Bankin Duniya.

Boris Johnson da Volodymr Zelensky

A jawabin da ya saba gabatarwa da dare Shugaba Zelensky ya bayyana Boris Johnson a matsayin abokin Ukraine na gaskiya, tare da yaba wa Birtaniya da Firaministan saboda taimaka wa kasarsa:

Ya ce “Boris (Johnson) na daga cikin wadanda ba su taba saurarawa ko ta dan lokaci ba kan su taimaka wa Ukraine.

Jagorancin Birtaniya wajen bai wa kasarmu taimakon da ya wajaba, musamman na kayan tsaro, tare kuma da jagoranci wajen sanya takunkumi abu ne da zai dawwama a tarihi.

A tarihin kare dimokuradiyya, a tarihin kare Turai. Har abada Ukraine ba za ta manta da alherin da Boris da Birtaniya suka yi mata ba” in ji shi

Volodymyr Zelensky ya kuma yaba da taron duniya na taimaka wa kasarsa da dala biliyan 11.

Ya yaba wa masu bayar da tallafin da suka hada da gwamnatoci da kamfanoni da bankuna da daidaikun jama’a, wadanda suka yi alkawarin tallafawa a taron da aka yi a Poland.

Leave a Reply