Bincike ya gano cewa Musulunci na ƙara karɓuwa a duniya fiye da kowanne addini
Daga Shafaatu Dauda Kano
Wani sabon rahoto da Cibiyar Bincike ta Pew ta fitar ya nuna cewa addinin Musulunci shi ne ke ƙara yaduwa da sauri fiye da duk wani addini a faɗin duniya tsakanin shekarun 2010 zuwa 2020
Rahoton da aka wallafa mai taken “Global Religious Landscape” ya bayyana cewa wannan ci gaba ya samo asali ne sakamakon yawan haihuwar da ke tsakanin Musulmai da kuma matakin shekaru ƙanana da ke cikin al’ummar Musulmi.
A cewar rahoton, mata Musulmai na haifar yara kusan guda 2.9 kowacce mace, yayin da sauran mata da ba Musulmi ba ke da matsakaicin haihuwa guda 2.2.
Haka kuma, rahoton ya ce Musulunci ne kaɗai daga cikin manyan addinai da adadin mabiya ke ƙaruwa sosai, inda yawan masu karɓar Musulunci ke fiye da na masu fita daga addinin – akasin abinda ke faruwa a cikin Kiristanci da Hindu.
KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar kiristoci a Kaduna ta nemi a bawa ‘ya’yanta aiki a hukumar Hisbah
Ko da yake Kiristanci ke da mabiya sama da biliyan 2.3 a duniya, rahoton ya nuna cewa adadin ya ragu da kashi 1.8 cikin ɗari tun daga shekarar 2010.
Ƙasashen da suka fi fuskantar ƙarin yawan Musulmai sun haɗa da Indonesia, Pakistan da Najeriya — inda Musulunci ke da rinjaye tun da dadewa.
A bangaren wasu yankuna kuwa, musamman kamar Amurka, rahoton ya ce yawan mutanen da ba sa bin kowanne addini ya ƙaru da kashi 97 cikin ɗari a cikin shekaru goma da suka gabata.
A ƙasar China kuwa, kimanin mutane biliyan 1.3 ba su da alaƙa da kowanne addini, in ji rahoton da jaridar DAILY TRUST ta wallafa.