Bilicin ya sa na ji kamar an jefa ni a gidan yari’

0
279

Wata matashiya mai suna Ellen ta bayyana irin halin tasku da ta shiga saboda yunƙurin da ta yi na sauya launin fatarta.

A bidiyon, ta shedawa BBC cewa ta fara shafe – shafen ne lokacin da taga ƙuraje wato pimples sun fara fito mata, tana neman man da ze warkar dasu, ya kuma cire mata tabon da ƙurajen suka bari. A haka seta tsinsti kanta ta chanza kalar fatarta daga baƙa zuwa fara, kuma duk sanda ta dakata da shafe shafen, setaga bazata iya ba.

Ellen ta kamu da bilicin, ya zamar mata jiki.

Kazalika, ta ce lamarin ya saka ta ta ji kamar an kulle fatarta ne a gidan yari saboda matsalolin da ta fuskanta a lokacin da ta yi yunƙurin daina shafe-shafen.

Matashiyar mai shekara 22 ta ce duk da ta yi nasarar sauya launin fatar ta ta cikin sauri, bilicin ya tsofar da ita kuma ta zama kamar ‘yar shekara 40

Dole Ellen ta koma launin fatarta na asali don ta yi maganin ƙuraje da tabo-tabo da suka cika mata fuska.

Leave a Reply