Bayan Shekaru tara, Sojoji sun sake kuɓutar da ‘yar makarantar Chiɓok guda ɗaya

3
261

Dakarun Bataliya Taskforce 114 dake Bita a jihar Borno sun sake kuɓutar da wata ‘yar makarantar Sakandiren Chiɓok guda ɗaya wadda aka sace tare da wasu sauran ɗalibai a ranar 14 ga Afrilu, 2014.

A ranar 21 ga watan Afrilun 2023 ne sojojin suka ceto Hauwa Maltha mai shekaru 26 mai lamba ta biyu a jerin ‘yan matan makarantar Chiɓok da aka sace tare da jaririnta mai shekaru uku a lokacin da suke gudanar da wani samame a Lagara.

Ta fito daga ƙabilar Kibaku dake Jila a ƙaramar hukumar Chiɓok ta jihar Borno. Yayin da take tsare, Hauwa ta yi aure a Gulukos da wani Salman, mai ɗaukar hoto ga marigayi shugaban ta’addanci, Shekau.

Daga baya Salman ya rasu a tafkin Chadi. Daga nan sai Hauwa Maltha ta sake yin aure da wani Malam Muhammad a garin Gobara ta haifa masa ‘ya’ya biyu.

KU KUMA KARANTA: An sake ceto ƴan matan Chibok biyu a Jihar Borno

An kuma kashe Malam Muhammad, mijin ta na biyu a Ukuba da ke dajin Sambisa a lokacin da aka yi artabu tsakanin ‘yan ƙungiyar JAS/ISWAP.

Tun bayan ceto Hauwa, wadda ita ma tana ɗauke da cikin kimanin wata takwas da sati biyu, an yi mata cikakken binciken lafiya tare da jaririnta.

Bayan an farfaɗo da su yadda ya kamata, Hauwa da jaririyarta, Fatima, za a miƙa su ga gwamnatin jihar Borno domin ci gaba da gudanar da rayuwa.

3 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here