Bai kamata ana ɗaukar mabuƙata hotuna a lokacin da ake ba su sadaka ba – Dakta Jameel Sadis

0
37
Bai kamata ana ɗaukar mabuƙata hotuna a lokacin da ake ba su sadaka ba - Dakta Jameel Sadis

Bai kamata ana ɗaukar mabuƙata hotuna a lokacin da ake ba su sadaka ba – Dakta Jameel Sadis

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Abu ne maifi sosa zuciya gannin yadda ake daukar Video da hotunan mutane a cikin yana yin kaskanci lokacin da ake raba musu sadaka.

KU KUMA KARANTA:Daga fara Azumin Ramadan, mutane 11 ne suka musulunta a wajen tafsirin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Dr Jameel Muhammad Sadis babban malami dake wa’azantarwa, ya bayyana rashin jindadinsa game da yadda mawadata ko Yan siyasa ke daukar hotuna ya yin da suke taimakawa masu bukata.

Abu ne mai matukar sosa zuciya ganin yadda ake daukar video na musamman da hotunan mutane a cikin yanayi na kaskanci lokacin da ake raba musu sadaka.

Bawan Allah! Ka nemi yardar Allah. Allah yana gani kuma ba ya mantuwa. Shi ne zai biya ka ba mutane ba. Kar ka nemi yabon me yabo in ba Allah ba.

Bawan Allah! Ko dan Allah ka bayar, ai kare mutuncin mai karbar sadakar wani abu ne mai muhimmacin gaske. Tambarin hotonka a kan buhun shinkafa ba shi Allah ke bukata ba. Samuwar tambarin neman yardar Allah a zuciyarka shi Allah ke so.

Sadakarka shuka ce. Yi mata kyakkyawar shuka domin haduwa da ita a qabarinka ko a filin Qiyama.

Leave a Reply