Ba ni da gida a Landan, bani da sha’awar tara dukiya- Buhari

0
276

Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, ya shaida wa Sarki Charles III na Burtaniya cewa ba shi da gida a ƙasar.

Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin ziyararsa a Birtaniya a sa’ilin da yake amsa wata tambaya a wani faifan bidiyo mai tsawon daƙiƙa 25 da mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Tolu Ogunlesi ya wallafa a shafin Twitter.

Shugaban ya ce, “Lokacin da shi (Sarki Charles III) ya tambaye ni ko ina da gida a nan (Birtaniya), sai na ce a’a, ko a Najeriya, wa’danda nake da su, su ne waɗanda na gina kafin in shiga gwamnati.

“Ba ni da sha’awar tara dukiya a ko’ina. Nafi jin daɗi da samun ‘yanci idan ban tara abubuwa da yawa ba,” in ji shi.

Leave a Reply