Ba mu yarda da ƙarin farashin man fetur ba – Marasa rinjaye a majalisar wakilai

0
46
Ba mu yarda da ƙarin farashin man fetur ba - Marasa rinjaye a majalisar wakilai

Ba mu yarda da ƙarin farashin man fetur ba – Marasa rinjaye a majalisar wakilai

Kwamitin ƙolin marasa rinjaye a majalisar wakilan Najeriya ya yi tir da sanarwar -bayan nan da kamfanin man fetur ɗin Najeriya (NNPCL) ya yi ta ƙara farashin man fetur.

A sanarwar da Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar, Kingsley Chinda, ya fitar a ranar Alhamis, ta ruwaito kwamitin ƙolin marasa rinjaye na cewa, bawai kawai lamarin ya zo ne a lokacin da bai dace ba, a’a ƙarin yin burus ne da irin mummunan halin matsin tattalin arziƙin da al’umma ke fama da shi ne a faɗin Najeriya.

Kwamitin ƙolin ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta ɗaukar mataki tare da janye abin da ya ƙira da ƙarin farashin man fetur ‘maras dalili’.

KU KUMA KARANTA:Mun gano haramtattun hanyoyin da ake satar man fetur a Najeriya – NNPC

Sanarwar ta kara da cewa, “a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin tattalin arzikin da ba a taba gani ba, da suka hada da hauhawar farashin kayayyakin masarufi da rashin ayyukan yi da faduwar darajar naira, karin farashin man fetur ba zai yi komai ba illa kara ta’azzara muwayacin halin da talakan Najeriya ke ciki”.

A Talatar da ta gabata ne kamfanin man NNPCL ya kara farashin litar man fetur daga naira 568 zuwa naira 855 ko 897 (ya danganta da nisan wuri), duk kuwa da matsalar karancin man da ta jima tana addabar Najeriya.

Sabon karin farashin fetur din na zuwa ne bayan da kamfanin NNPCL ya amince da cewar masu sayar masa da man na bin sa bashin daya haura dala bilyan 6.

Leave a Reply