Ba don kuɗi na auri mijina ba – Hafsat Ɓarauniya

0
606

Anata yaɗa jita-jita a masana’antar Kannywood cewa fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Hafsat Idris ta auri Mukhtar Alhassan a ranar 26 ga watan Fabrairu, 2021, ta yi hakan ne saboda saurayin yana da arziƙi fiye da kima.

Hafsat Idris

Wakilin Neptune da ya halarci ɗaurin auren Rukayya Dawayyah da Ismail Na Abba Afakallah, ya kawo mana rahoton cewa jarumar wadda ‘yar asalin jihar Sokoto ce har yanzu tana jin zafin tsegumin da ƙawayenta a masana’antar ke yi na cewa ta auri saurayin ne saboda kuɗi.

Hafsat ɓarauniya wacce ta taɓa aure, ta auri wani a garin Shagamu inda iyayenta suke yanzu haka. Ta shafe shekara tara a gidan aure kafin su rabu, Allah ya albarkace su da ’ya’ya mata guda biyu kyawawa da namiji ɗaya kafin ta koma Kano ta ci gaba da sana’ar film a Kannywood.

A tattaunawarta ta farko da ta yi a kafafen yaɗa labarai, lokacin tana sabuwar zuwa Kano, ta shaida wa wakilin Neptune Prime cewa ta shiga harkar fim ne bayan ta haɗu da wani ɗan Kannywood a kasuwar GSM, Kano, ta shaida masa sha’awarta ta shiga film.

Ya karɓi lambarta ya yi alƙawarin haɗa ta da wasu furodusoshi.

“Na jira tsawon wata shida kafin na ji kira daga gare su, sai suka haɗa ni da Ali Nuhu wanda ya fito dani a fim ɗin Ɓarauniya a matsayin jaruma me jan ragamar shirin.

“Alin ya yi min wasu tambayoyi kuma ya gamsu matuƙa da amsoshina, da kuma salon acting dina bayan da muka fara daukan wasan” inji ta.

Tun daga wannan lokacin Hafsat Idris ta kasance jarumar fim a Kano, kafin ta yi aure a shekarar da ta gabata wanda ta yi a rana irin ta yau da Aisha Aliyu Tsamiya, wadda itama hamshaƙiyar attajira ce kuma kyakkyawar jaruma ce wacce a yanzu haka ke gudanar da kayyakin kasuwanci na miliyoyi a Khairat Plaza a hanyar BUK.

A yanzu Hafsat ta zama cikakkiyar matar aure, a shekarar da ta gabata ‘yarta ta farko ta yi aure, wasu abokan aikinta sun mayar da taron abin gulma saboda irin wankan gwal ɗin da tayi a ranar, inda ake zargin sabon mijinta Alhassan Muktar wanda yake ɗan marigayi Sani Abacha ya saya mata, wai kuma ta auri saurayin ne saboda kudinsa.

Duk da cewa tana sana’ar siye da siyarwa na abubuwa daban daban, kuma a mafi yawan lokuta, tana fita ƙasashen waje, ta shaida wa abokanta cewa mijinta ba ya da alaƙa da dangin Abacha, kuma ta aure shi ne saboda tana sonsa, kuma yana ba ta ƙwarin gwiwar gudanar da harkokin kasuwancinta, duk da cewa ta daina wasan kwaikwayo.

Leave a Reply