Arsenal ta doke Fulham 2-1 a wasan mako na huɗu a gasar Premier League

0
543

Arsenal ba ta taba rashin nasara a hannun Fulham a gida ba. Kungiyoyin biyu sun je hutu ba tare da an ci kwallo ba – daga baya Fulham ta zura ɗaya a raga ta hannun Aleksandar Mitrovic, na huɗu da ya ci kenan a bana.

Daga baya ne kyaftin din Arsenal, Martin Odegaard ya farke, sannan Gabriel Magalhaes ya ƙara na biyu.

Wasa na huɗu da Arsenal ta yi nasara a jere a kakar bana kenan, tana nan a mataki na ɗaya a kan teburi da maki 12.

Karo na 31 da Arsenal ta fuskanci Fulham a gida ba tare da rashin nasara ba a dukkan fafatawa da ta yi da kungiyar.

Wannan shi ne wasa na 100 da Mikel Arteta ya ja ragamar Arsenal a Premier League – ya yi nasara 53 da canjaras 16 da shan kashi a wasa 31.

Karo na 34 da Gunners ta fuskanci sabuwar kungiyar da ta hau Premier League tun bayan da ta yi rashin nasara a hannun Newcastle da ci 1-0 a Nuwambar 2010.

Cikin wasa 34 da Arsemal ta yi da sabbin kungiyoyin da suka hau babbar gasar tamaula ta Ingila, Gunners ta ci 29 da canjaras biyar.

Leave a Reply