Arewacin Najeriya zai bayyana matsayarsa kan zaɓen 2027 – Hakeem Baba-Ahmed

0
140
Arewacin Najeriya zai bayyana matsayarsa kan zaɓen 2027 - Hakeem Baba-Ahmed

Arewacin Najeriya zai bayyana matsayarsa kan zaɓen 2027 – Hakeem Baba-Ahmed

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Hakeem Baba-Ahmed, tsohon mai bai wa Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima shawara kan harkokin siyasa, ya yi gargadin cewa Arewacin Najeriya na iya daukar matsaya mai tsauri dangane da makomar siyasar yankin idan aka ci gaba da watsi da koke-koken yankin.

A cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Baba-Ahmed ya bukaci ‘yan Arewa da su ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya tare da lura da “makaryata” da ke aiki don raunana yankin.

“Arewacin Najeriya za ta tsaya ta kare kanta, wallahi,” a cewar sa.

KU KUMA KARANTA:An dawo da tsohon jami’in ‘Anti-Daba’ Gwadabe don kakkaɓe ‘yan daba a Kano

“Ya kamata Arewa ta yi hattara sosai, ta guji ‘yan siyasa na cin amana da kuma duk wani abu da zai kawo rabuwar kai.”

Ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin dukkan kabilu da addinai na Arewacin Najeriya, ciki har da Musulmi, Kiristoci, Fulani, Baju da Mangu.

“Yanzu kun gane, babu dan siyasa da zai zo ya ce, ‘Ina ‘yan Arewa, ku biyo ni.’ Kai wane ne?” ya tambaya.

Leave a Reply