Arewa ta Tinubu ce, ranar zaɓe muke jira – Ganduje

0
589

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ɗaukacin jihohi ɗan takarar jam’iyyar mai mulki ta APC Ahmed Bola Tunibu za su zaɓa a zaɓen 2023, kuma al’ummar yankin sun shirya tsaf, lokaci suke jira su kaɗa ƙuru’arsu, inda ya buƙaci ‘yan Arewa mazauna Legas suma su fito ayi tafiyar Tunibu da su.

Daga Hagu Kashim Shattima, sai sarkin Hausawan Legas Alhaji Aminu Yaro Dogara da Sarkin Fulanin Legas Alhaji Mohammed Bambado sai Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje

Abdullahi Gabduje ya shaida haka ne a jiya Laraba a lokacin da ya ziyarci al’ummar Hausawa da ke zaune a kasuwar Alaba Rago tare da rakiyar gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu da mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar APC Sanata Kashim Shattima inda yace sun yin rangadi ne domin bai wa ‘yan Arewa mazauna kudu bushara.

Mun zo muku da albishir, da kyakkyawan labari, idan ana maganar Arewa, to ta Tunibu ce, mun riga mun gama da wannan babin mun kuma rufe shi, ranar zaɓe kawai muke jira, don haka muna fatan kuma al’ummar jihar Legas zaku yunƙuro a tafi tare da ku.

JiGwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da Sarkin Fulanin Legas Alhaji Mohammed Bambado

” Kano zata bai wa Tunibu ƙuri’u mafi yawa fiye da ko wace jiha, don haka kuma mutanen Legas muna ƙalubalantar ku da kuyi mana alkawarin zaku ɗara Kano a yawan ƙuri’un da zaku kaɗa wa Tunibu” inji shi.

A nasa jawabin, Sanata Kashim Shattima cewa yayi, mutanen Arewa zasu ramawa kura aniyarta ne a zaɓen 2023, yace lokaci ne da ‘yan Arewa zasu saka wa Tunibu da alkahiaran da yayi masu na gina manyan ‘yan siyasa a Arewa da yayi, tare da basu gudunmawa wajen cimma manufofin su na siyasa.

” Ina so na faɗa maku mahimmancin zaɓen 2023, mu a Arewa lokaci ne na rama wa kura aniyarta, domin a zaɓukan da suka gabata Tunibu ya taimakawa ‘yan takaran Arewa, a zaɓukan shekarar 2015 da 2019, wanda hakan ne ya bai wa shugaba Buhari Nasara.

A lokacin ziyarar tasu a Legas, Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Kashim Shattima sun ƙaddamar ofishin yaƙin neman zaɓen Tunibu/Shattima da na gwamnan Legas wanda shugaban ‘yan Arewa ‘yan jam’iyar APC Alhaji Sa’adu Yusuf Gulma ya samar sun kuma ziyarci fadar Sarkin Fulanin Legas Alhaji Mohammed Bambado tare da Sarkin Hausawan Legas Alhaji Aminu Yaro Dogara.

Leave a Reply