APC Za Ta Yi Babban Taronta Na Kasa A Watan Gobe

0
279

Daga Rabo Haladu

Jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa za ta gudanar da babban taronta na ƙasa ranar 26 ga watan Fabrairu.

Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin riƙon jam’iyyar wanda kuma da kwamitin shirya taron jam’iyyar ne ya bayyana haka a Abuja ranar Talata.

Wasu jaridu sun rawaito cewa Mai Mala ya sanar da hakan ne a wajen taron da matan jam’iyyar ke gudanarwa a Abuja.

Gwamnan ya kara da cewa ƙidayar ƴaƴan jam’iyyar da aka gudanar a a bara ya sa sun gano cewa suna da mambobi miliyan 40.

Leave a Reply