Ango ya kai ƙarar Amaryarsa Kotu kan zargin ta sace masa wayoyin hannu

0
114

Ango ya kai ƙarar Amaryarsa Kotu kan zargin ta sace masa wayoyin hannu

Daga Jameel Lawan Yakasai 

Wani ango mai suna Usman Ali ya gurfanar da amaryarsa Maryam a gaban kotun shari’ar Musulunci da ke garin Jaba a Kano, bisa zargin ta da satar masa wayoyin hannu guda uku da suka kai kimanin naira dubu 65,000.

Yayin zaman kotun, Maryam ta musanta laifin, tana mai cewa ta biya kudin mota daga Abuja zuwa Kano ne domin tserewa daga dukan da mijin nata ke yi mata, wanda hakan ya sa ta dawo wajen iyayenta a Kano.

Angon ya kuma shigar da kawayenta 3 a Kotun bisa zargin suna hure mata kunne tana tafiya yawo.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta Sanya dokar Noma ta shekara Biyar ga duk Wanda aka kama da satar waya

Mai shari’a, Alkali Ustaz Rabiu Yahaya, ya bayar da belin Maryam, tare da sanya ranar 15 ga watan Yulin da mu ke ciki domin ci gaba da wannan shari’ar.

Leave a Reply