Ana zargin wani matashi da ƙaninsa sun yi wa almajiri yankan rago a Adamawa

0
38
Ana zargin wani matashi da ƙaninsa sun yi wa almajiri yankan rago a Adamawa

Ana zargin wani matashi da ƙaninsa sun yi wa almajiri yankan rago a Adamawa

Rundunar ’yansandan jihar Adamawa ta cafke wasu mutane biyu, waɗanda yaya da ƙani ne Aliyu Abdulmalik da Ibrahim Abdulmalik kan zargin yanke kan wani almajiri ɗan shekara 10, Abdallah Lawali.

Bayanai sun ce ’yan’uwan junan biyu sun aikata wannan ta’asa ce a ranar 7 ga watan Maris a unguwar Sarkin Yamma da ke Ƙaramar Hukumar Jada.

Sanarwar da rundunar ’yan sandan ta fitar ta ce an kama ababen zargin ne da gangar jikin almajirin a cikin wani buhu, yayin da aka ƙwaƙulo kansa a cikin wani rami da suka binne a harabar gidansu.

KU KUMA KARANTA:‘Yansanda sun kama jami’an NDLEA 2 kan zargin kisan wata budurwa a Kano

Rundunar wadda ta ce yanzu haka bincike ya kankama a kan lamarin, ta kuma bayyana cewa ababen zargin sun yi iƙirarin aikata laifin da suka alaƙanta da sharrin shaiɗan.

Kwamishinan ’yan sandan jihar CP Dankombo Morris, ya tabbatar da cewa za a yi adalci a lamarin, yayin da yake kira ga al’umma da su kasance masu lura da miƙa rahoton duk wani motsi da su aminta da shi ba zuwa ofishin mahukunta mafi kusa.

Leave a Reply