Ana zargin matasa 3 da laifin yiwa wasu matan aure duka a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Kotun Majistiri mai zaman kanta akan titin Zungeru, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Faruƙ Umar Ibrahim, ta sanya ranar 19 ga watan gobe, don ci gaba da sauraron shaidu a ƙunshin ƙarar da ‘yansanda suke wa wasu matasa uku.
Ƙunshin zargin ya bayyana cewar, matasan sun haɗa baki sun doki wata mata da shebur ɗin kwasar ƙasa, yayin da mai gidanta ya kawo mata ɗauki shima suka rufe shi da duka har suka karya masa ƙafa, ko dayake tun a baya sun musanta zarge-zargen.
KU KUMA KARANTA: Ana zargin Amarya da yiwa angonta yankan Rago a Kano
A zaman kotun a ranar Talata, lauyar Gwamnati Hajara Ado Sale ta gabatar da shaidu biyu an kuma ɗage sauraron jin shaidun zuwa ranar 19 ga watan gobe.