Ana zargin kwamandan Hisbah a Kano da karɓar cin hancin Naira Dubu 50

0
134
Ana zargin kwamandan Hisbah a Kano da karɓar cin hancin Naira Dubu 50

Ana zargin kwamandan Hisbah a Kano da karɓar cin hancin Naira Dubu 50

Daga Jameel Lawan Yakasai

Wata mai ta bawa Kwamandan Hisbah a ƙaramar hukumar Minjibir dake Kano cin hancin kuɗi, kimannin Naira Dubu Hamsin sakamakon kamata da hukumar ta yi da zargin laifin tara Maza da Mata a gidan ta.

Sai dai kwamandan Hisban Malam Abdullahi kyauta ya hau teburin naƙi kan da’awar matar na karɓar cin hanci domin gudanar da waɗancan taruka.

KU KUMA KARANTA: Hisbah a Kano ta ja kunnen Amare da su daina zaman Majalisa idan mazajen su sun fita

‎Matar mai suna Hajiya yabi dake zaune a unguwar yamma a ƙaramar hukumar Minjibir ta aikewa da kwamandan Hisban mai suna Abdullahi kyauta turmin Atamfa da kudi naira dubu hamsin domin ya sahale mata gudanar da tarukan da suka saɓawa Shari’ar musulunci.

‎Tuni dai rundunar ta hisbah a ƙaramar hukumar ta Minjibir ta dukufa domin kauda ɓarnar da wannan hajiya ke tafkawa a yankin.

‎Wannan kuma na zuwa yayin da Al’ummar yankin ke Allah wadai ga irin ta’asar da hajiyar ke haifarwa a garin, inda suka zargi wasu da ba a kai ga gano ko su waye ba ke dafawa hajiya Yabi.

Leave a Reply