Ana zargin jami’an hukumar Hisba ta jihar Katsina da cin zarafin wata mata
Daga Shafaatu Dauda Kano
Ma’aikatar dake kula da harkokin Mata ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta ƙaddamar da bincike kan zarge zargen da ake yi wa jami’an hukumar Hisbah na cin zarafin wata Mata a jihar
A dai Makon jiya ne aka riƙa yaɗa hirar da aka yi da wata Mata inda ta zargi jami’an na Hisbah da lakaɗa Mata duka, lamarin da ya kai ga karya Mata ƙafa da lahanta mata kunne.
KU KUMA KARANTA:Hisbah a Kano za ta fara kamen masu hira da mata a cikin mota
Neptune prime Hausa ta rawaito cewa tuni Ma’aikatar harkokin Mata ta jihar ta fara gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa jami’an na Hisbah, tana mai ƙara wa da cewa za ta yi binciken bisa gaskiya kuma za a yi shi a bayyane.
Dama dai an daɗe ana zargin hukumar da amfani da ƙarfi fiye da kima da duka yayin kame da tsare masu laifi, sai dai hukumar ta sha musanta haka inda ta ke cewa waɗanda ke goyon bayan aikata laifi ne ke yaɗa haka.