An zaɓi Robert Prevost a matsayin sabon fafaroma

0
133
An zaɓi Robert Prevost a matsayin sabon fafaroma

An zaɓi Robert Prevost a matsayin sabon fafaroma

Daga Ibraheem El-Tafseer

Fadar Vatican ta sanar da cewa Robert Prevost ne sabon fafaroma, wanda zai maye gurbin Fafaroma Francis.

Shi ne fafaroma na farko daga ƙasar Amurka wanda zai jagoranci cocin na Katolika na duniya.

Zai yi amfani da sunan Leo a muƙamin wanda shi ne fafaroma na 14 da ya yi amfani da sunan (Pope Leo XIV).

Sabon Fafaroman mai shekara 69 ya shafe shekaru yana ayyukan addini a ƙasar Peru.

A watan Satumban 2023 aka naɗa shi a muƙamin babban limamin Cocin Katolika wato ”Cardinal’.

Ana kallon Robert Prevost a matsayin mutum mai matsakaicin ra’ayin.

KU KUMA KARANTA: Paparoma Francis ya yi Alla-wadai da matakan Sojin Isra’ila a Gaza

An ayyana zaɓarsa a gaban dubban al’ummar da suka halarci fadar Vatican domin shaida zaɓen sabon fafaroman.

Dandazon mutanen sun ɓarke da sowa a lokacin da farin hayaƙi a bayyana wani bututu da ke saman Babban Cocin Kotolikan da ke alamta zaɓar sabon fafaroman.

Manyan limamanin Cocin masu muƙamin Cardinal ne ke zaɓar fafaroma, sannan sai an samu kashi biyu bisa uku na manyan limaman kafin a ayyana wanda ya yi nasara.

A jawabinsa na farko bayan zaɓarsa, Fafaroma Leo 14 ya yi kira da mabiya ɗariƙar Katolika su yi aiki tare ta hanyar amfani da tattaunawa don haɗa kan al’ummar duniya ta hanyar samar da zaman lafiya.

Leave a Reply