An tsinci gawar ƙananan yara 5 cikin wata mota ajiyayya

0
54
An tsinci gawar ƙananan yara 5 cikin wata mota ajiyayya

An tsinci gawar ƙananan yara 5 cikin wata mota ajiyayya

Daga Shafaatu Dauda Kano

Rundunar ‘yansandan jihar Nasarawa ta bayar da umarnin gudanar da bincike akan dalilin da ya sanya aka samu rasuwar wasu ƙananan yara su 5, a cikin wata motar da take ajiye sakamakon dena yin amfani da ita. Kwamishinan ‘yansandan jihar Shetima Jauro-Mohammed, ne ya bayar da umarnin gudanar da binciken, bayan samun gawar yaran a yankin Agyaragu, dake karamar hukumar Obi.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar Nasarawa SP Rahman Nansel, ne ya sanar da hakan a yau litinin lokacin da yake yin jawabi a Lafia.

KU KUMA KARANTA:‘Yansanda a Jigawa sun kama ango da abokansa bayan mutuwar amarya

Nansel, yace an samu gawarwakin yaran a cikin motar data lalace wadda aka ajiye a gidan wani mutum mai suna Abu Agyeme, yana mai cewa kwamishinan yan sandan ya bayar da umarnin gabatar da babban binciken dalilin mutuwar yaran, tare da bayyana jimami da takaicin samun labarin lamarin, inda ya mika sakon ta’aziyyar sa ga iyayen mamatan.

Bayan haka rundunar yan sandan ta nemi iyaye su rika sanya idanu akan ababen hawan da suke ajiyewa a gida sakamakon lalacewa don gujewa faruwar irin wannan abu.

Leave a Reply