An samu budurwar data ɓata daga Legas, a jihar Bauchi

0
564

Data Fatima GIMBA, Abuja

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta ce an gano matashiyar ‘yar shekara 17, Mildred Joshua Ebuka da ta ɓace a Legas ranar Alhamis 25 ga watan Agusta, a Bauchi.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a ta ce yarinyar ta shiga motar bas ne da ke kusa da gidansu da ke Victoria Island (V.I) domin kai wa ƙawar innarta Hular gashi wato ‘Wig’, kuma daga nan ne ta ɓata.

“Ta fito daga Legas kuma tana jin Turanci sosai. Sanye da riga shiriya da wando mara nauyi, fara ce, kuma babu tsagu ko zane a fuskar ta.” kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Mohammed Wakil ya faɗa.

A wani rubutu da rundunar ‘yan sandan Bauchi ta wallafa a shafinta na Twitter, ta sanar da iyayen yarinyar inda ta ke.

“Muna matuƙar godiya ga ALLAH Madaukakin Sarki da Ya bama rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ikon gano iyayen (Mildred Joshua Ebuka), ba sunanta na gaskiya ba, sunanta Jenifer Joshua Anga, kuma a halin yanzu zata haɗu da iyayenta cikin ƙoshin lafiya. Mungode ma masu kishin ƙasa,” kamar yadda aka wallafa a shafin Twitter.

Da yake magana da gidan Talabijin na Channels, SP Wakil ya ce, iyayenta na kan hanyarsu ta zuwa Bauchi yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Ya ce matashiyar an same ta ne a tashar mota, kuma wani matashi nagari ne ya kaita gurin ‘yan sanda, saboda ta kasa gane inda take.

Leave a Reply