An kwashe ragowar mahajjatan Yobe 210 zuwa ƙasa mai tsarki

0
144
An kwashe ragowar mahajjatan Yobe 210 zuwa ƙasa mai tsarki

An kwashe ragowar mahajjatan Yobe 210 zuwa ƙasa mai tsarki

Daga Ibraheem El-Tafseer

A yau Litinin aka kammala tantance ragowar Mahajjatan jihar Yobe 210 zuwa ƙasa mai tsarki, Saudiyya. Shugaban hukumar aikin Hajji na jihar Yobe Alhaji Mai Aliyu Usman ne ya jagoranci mahajjatan.

Rukunin waɗannan Alhazai waɗanda suka tashi a yau ɗin su ne rukuni na ƙarshe, a cikin adadin mutanen da suka ɗauki aniyar sauƙe farali a wannan shekarar a jihar Yobe.

KU KUMA KARANTA: Maniyyata 200 kacal suka biya kuɗin hajji a Taraba

Amirul Hajji Na Jihar Yobe kuma Mai Martaba Mai Tikau Alhaji Abubakar Muhammadu Ibn Grema ya yi jawabin bankwana tare da yi musu tunatarwa kan haƙƙoƙin da ya rataya a wuyansu domin tabbatar da ibadarsu karɓaɓɓiya, sannan ya yi ƙira garesu da su kyautata niyya sannan su bawa aikin Hajjin fifiko a dukkan lamurransu.

Leave a Reply