An kubutar da Ƴan Najeriya 13 da akayi Safararsu zuwa kasashen ketare
Daga Shafaatu Dauda Kano
Hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NIDCOM), ta karɓi wasu ƴan ƙasar 13 da akayi safararsu zuwa ƙasashen Ghana da Mali.
Shugabar hukumar, Abike Dabiri-Erewa, ce ta sanar da hakan a yayin da take tarbar waɗanda abin ya shafa da suka haɗa da ƴan mata 12 da yaro 1 ɗan shekara biyar, a cewar sashen Hausa na BBC.
KU KUMA KARANTA:An ƙaddamar da shiri kan take haƙƙin yara a Najeriya
Ƴan matan da aka ceto sun ce an yi musu wayo ne tare da tilasta musu shiga karuwanci, bayan an yaudare su da cewa za a samo musu aiki a Ghana da Mali, baya ga cin zarafin su da wadanda suka yi safarar tasu suka yi.
Matsalar safarar al’umma ta hanyar yaudarar su da cewa za a samo musu aiki a ƙasashen waje ya daɗe yana addabar ƙasar, inda ko a ƴan watannin baya an sami nasarar dawo da wasu matasa daga Ghana waɗanda aka tilastawa yin laifuka ta intanet.