An kashe ƙasurgumin ɗan fashin da ‘yansandan Kano ke nema, Baba Beru
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da Mutuwar Halifa Baba Beru, a wani artabu da ya gudana tsakanin Jami’an Yan sanda da wasu gaggan yan Daba a Unguwar Gwammaja.
Sanarwa da Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar yace, yan sanda sun kai dauki unguwar Gwammaja, lokacin da Halifa Baba Beru ya hada wasu yan daba suna tayar da hargitsi a cewar sanarwar.
KU KUMA KARANTA:Kotu ta yanke hukuncin rataye wani mutum mai laifin fashi da makami
Jaridar Neptune Prime ta Rawaito cewar Kiyawa na cewa yayin artabun Halifa Baba Beru da wasu yan daba sun raunata wasu daga cikin jami’an Yan Sanda, wanda aka kaisu asibiti domin duba lafiyarsu yayinda kuma likitoci suka tabbatar da cewa Halifa Baba Beru ya mutu.
Rundunar Yan Sandan Jihar kano ta bayyana cewa, zata binciko sauran wadanda suke tayar da rikici a unguwar ta Gwammaja, domin hukunta su harma tayi gargadin cewa Kwamishinan Yan Sandan jihar kano CP Ibrahim Adamu Bakori ba zai lamunci tayar da hankalin Alumma ba acewar Sanarwar.