An kama waɗanda suka kashe jami’in KAROTA a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Hukumar Kula da zirga Zirgar ababen hawa ta jihar kano KAROTA, ta sanar da kama waɗanda suka kashe jami’in ta da wuƙa a lokacin da yake bakin aiki.
Daga cikin wadanda aka Kama bisa zargin hallaka jami’in akwai direban wata babbar mota da yaron sa, sai kuma wani jami’in Soja.
KU KUMA KARANTA:Direban mota ya kashe jami’in Karota a Kano
Shugaban hukumar Injiniya Faisal Mahmoud, ya ce zasu yi bakin kokari wajen tabbatar da adalci ga jami’in da aka hallaka musu.
Idan za’a iya tunawa a wannan mako ne aka samu labarin cewa wasu mutane sun yiwa jami’in KAROTA kisan gilla lokacin da yake bakin aiki.