An kama mutane 4 kan zargin kashe ɗalibar jami’a a Kogi

0
55
An kama mutane 4 kan zargin kashe ɗalibar jami’a a Kogi

An kama mutane 4 kan zargin kashe ɗalibar jami’a a Kogi

‘Yansanda sun kama mutane 4 da ake zargi da hannu a kisan wata ɗalibar jami’ar tarayya da ke Lokoja, jihar Kogi.

Ana zargin wani matashi da sace ɗalibar mai shekaru 17 da ke aji na farko a jami’ar, inda kuma ya kashe ta.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansanda a jihar, SP Williams Ovye-Aya, ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai.

Onye-Aya ya ce babban wanda ake zargin ya hada kai da abokanan sa uku wajen aikata laifin.

“Jami’an ‘yansandan Najeriya dake sashin binciken manyan laifuka a jihar Kogi, sun kama Jeremiah Paul-Awe na karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a ranar 11 ga watan Satumba.

” Paul shi ne ya sace ɗalibar kuma ya kashe ta.

KU KUMA KARANTA:An ceto ɗaliban jami’ar Jihar Kogi da aka sace

“Mun karɓi ƙorafi daga Stephen Oluwoyo cewa ‘yarsa ta ɓata kuma baya samun ta.

”Mahaifin nata ya ƙara da cewa ya samu saƙon waya daga wata sabuwar lamba cewa an yi garkuwa da ‘yarsa kuma ana neman kuɗin fansa”, inji shi.

Rundunar ‘yansandan ta ce waɗanda ake zargin sun amsa laifin su.

Sannan za a gurfanar dasu gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Leave a Reply