An kama Ƴar Najeriya meyin Safarar Mutane zuwa Ƙasashen waje

0
51
An kama Ƴar Nigeria meyin Safarar Mutane zuwa Ƙasashen waje

An kama Ƴar Najeriya meyin Safarar Mutane zuwa Ƙasashen waje

Daga shafaatu Dauda Kano

Rundunar ‘yan sandan kasar Australia sun kama wata mata ‘yar Najeriya mazauniyar ƙasar mai suna Binta Abubakar, bisa zargin safarar mutane da kuma tilasta wa wasu dalibai daga ƙasar New Guinea yin aiki ba tare da an biya su ba.

Binta Abubakar mai shekaru 56, an kama ta ne a Filin Jirgin Sama na Brisbane, a ranar Laraba, a lokacin da ta iso daga Papua New Guinea, inda ake zargin ta tafi gudanar da harkokinta.

An kama ta ne bayan wani bincike da ya ɗauki tsawon shekaru biyu da aka fara tun a watan Yulin 2022, bayan samun bayanai daga ‘yan sandan jihar Queensland.

A cewar hukumar ‘yan sandan ƙasar wani gungun matasa daga Papua New Guinea da aka ce sun zo Austaraliya domin karatu, sai aka tilasta musu yin aikin noma ba tare da albashi ba.

KU KUMA KARANTA: An kubutar da Ƴan Najeriya 13 da akayi Safararsu zuwa kasashen ketare

Rahotanni sun bayyana cewa matar ta yaudari akalla mutane 15 ‘yan tsakanin shekaru 19 zuwa 35 daga Papua New Guinea zuwa Austaraliya daga watan Maris 2021 zuwa Yuli 2023, ta hanyar kamfaninta mai suna BIN Educational Services and Consulting.

Shafin kamfanin yana tallata kansa da cewa yana bayar da tsarin zamani da cikakken kulawa a fannin ilimi, horo da kuma samar da aiki.

Sai dai hukumomin tsaro sun bayyana cewa abinda ke faruwa a gaskiya yana da matuƙar bambanci da yadda ake tallata kamfanin.

Leave a Reply