An kama ƙatti 3 da suka yima matar aure fyaɗe a gaban mijinta

0
492

An kama wasu garada uku da suka yi ma wata matar aure mai dauke da cikin watanni bakwai fyade a gaban mijinta a Jihar Kwara. 

Kamar yadda jami’an yaɗa labarai na Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) ya sanar, wannan mummunan lamarin ya faru ne a ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama a Jihar Kwara a makon jiya. 

Waɗanda aka kama din sune, Lawal Ibrahim, 25; Mohammed Issa, 19; da Ibrahim Ahmed, 20; ana zargin bayan fyaden da suka aikata, sun yi wa mijin matar fashi da makami.

Mai magana da yawun NSCDC a Jihar, Ayeni Olasunkanmi, ya ce ɗaya daga cikin wadanda ake zargin, Lawal, an kama shi ne a lokacin da yake ƙoƙarin siyar da wasu daga cikin kayan da suka sato a gidan ma’auratan. 

Bayanin ya bayyana cewa, “An kawo mana rahoton da ya ƙunshi fyade da fashi da makami  da aka aikata a ranar 5 ga Yuli, 2022 a ofishin NSCDC da ke ƙauyen Woro a Karamar Hukumar Kaiama a Jihar Kwara. 

“Waɗanda abin ya shafa da suka hada da matar aure mai dauke da cikin watan bakwai da mijinta, an auka masu ne a gidansu da ke Woro, inda suka yi wa matar fyade a gaban mijinta, tare da sace wasu daga cikin kayayyakinsu masu amfani. 

“Bayan samun wannan rahoton, sai muƙaddashin Kwamandan rundunar NSCDC, DCC Jonah Gabriel, ya tayar da runduna, tare da ba da umarnin a bi sawun ɓata garin domin a kamo su. 

“Jami’anmu sun yi nasarar damƙe Lawal Ibrahim, yayin da yake kokarin siyar da wasu daga cikin kayayyakin da suka sato. 

“Wanda aka kama din ya yi kirarin aikata laifin da ake zarginsa da aikatawa da bakinsa, yayin da bayanansa suka taimaka wajen kama sauran mutum biyu da ake zargi,”  in ji shi. 

Mr. Ayeni ya ce tuni suka gurfanar da wadanda suke zargin a gaban kotu a garin Kaiama bayan sun kammala bincike. 

Leave a Reply