An je taimakonsa ya yi hatsari, ashe ɓarawo ne, an samu kayan sata a hanunsa
Ya yi hatsari kusa da sakatariyar ƙaramar hukumar warji kawai sai kayan sata suka bayyana fili.
KULƁA NA ƁARNA…
Wannan mutum da kuke gani, dubunsa ta cika. Ya je ya sato wayar lantarki (electric cable) tsakanin garin Miya da ke karamar hukumar Ganjuwa da Warji.
Bayan ya sato wayar, cikin hukuncin Allah, yayin da yake kokarin ficewa da kayan sata ya yi hatsari a kusa da sakatariyar karamar hukumar Warji. Buhun da ke dauke da kayan ya fashe. Sai jama’a suka taru, nan ne aka gano cewa wayar lantarki ya sato ne daga jeji.
KU KUMA KARANTA:NSCDC a Yobe ta cafke mutane 17 kan aikata laifin sata
A halin yanzu, yana hannun Hukumar Tsaro ta NSCDC (Nigerian Security and Civil Defence Corps) ta karamar hukumar Warji.
Shaidun da suka gani da idonsu sun bayyana cewa mutumin dan garin Buran Kwari ne, daga gundumar Gabanga, karamar hukumar Warji.
Muna kira ga mahukunta da su zurfafa bincike don gano yadda yake tafiyar da wannan aika-aika, da kuma daukar matakin hukunci a kansa da duk wanda ke tare da shi.
Muna kuma Allah wadai da irin wadannan bata-gari da ke cutar da al’umma.