An hallaka matashi ƙanin fitaccen ɗan siyasa lokacin da yake zance wajen budurwarsa

0
590

A jiya Asabar wani matashin mai suna Ashiru Tofa ya gamu da ajalin sa, sanadiyyar daɓa masa wuƙa da aka yi kirji a garin Minna a jihar Naija.

Matashin ƙani ne ga fitaccen ɗan siyasa a cChanchaga na jihar, Hon. Jamilu Tofa, ya kuma rasa ransa ne a daidai kusa da ofishin yansanda na Area commander a lokacin da yaje zance wurin budurwar sa.

Ruhotanni sun ce ana zargin wani da suka haɗa nema ne ya yi masa aika-aikar, kuma kamin akai shi asibiti ya rasu.

Tuni aka yi jana’izarsa da safiyar yau Lahadi.

Marigayin

Leave a Reply