An Gudanar Da Liyafar Murnar Sabuwar Shekarar 2022 Ga Yan Jaridun Kaduna A Karo Na 8

0
242

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

SHUGABAN gidauniyar Farfado da Zaman Lafiya ta Najeriya (Peace Revival Foundation of Nigeria), Fasto Yohanna Buru ya yaba da rawar da kafafen yada labarai ke takawa musamman ‘yan Jaridun Jihar Kaduna wajen samar da zaman lafiya.

Da yake jawabi a wajen bikin sabuwar shekara a kungiyar ‘yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Kaduna, Buru ya bayyana cewa idan ba don irin taimako da gudunmuwar ‘yan Jaridu ba, toh da ba zasu tabbacin aiwatar aikin wa’azin zaman lafiya da suke ba.

Ya ce “Inda ba don irin gudunmuwa da taimakon Yan Jaridu ba wajen yada manufofinmu a irin wannan tafiyar ba, toh nadin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi mun da baiyu ba, toh amma saboda irin goyon bayan da kafafen yada labarai ke yi a Kaduna ne ya sanya hakan.”

A cewar Fasto Yohanna Buru, wannan shekarar ta 2022, ita ce shekara ta 8 da suke gudanar da bikin tare da ‘yan Jaridu a harabar Kungiyar ta NUJ dake Kaduna, kuma makasudin gudanar da liyafar cin abincin shi ne don nuna aminci bisa ga irin abin da ‘yan Jaridu ke yi domin samar da zaman lafiya a Najeriya, baya ga jaddada cewa ‘yan jarida sun cancanci karramawa.

“Ba shakka, sabbin shugabannin cibiyar Kungiyar ta NUJ da salon Jagorancin suna aiki mai kyau kuma ina iya ganin bambanci a fili, domin yanayin harabar wajen yana da kyau.” Inji Buru.

Da take jawabi a wajen taron, shugabar Kungiyar kuma mace ta farko a reshen Kaduna, Hajiya Asma’u Yawo Halilu, ta kara da bada tabbacin ga masu ruwa da tsaki kan kudirin ta na ganin an samar da gaskiya da adalci wajen samar da zaman lafiya.

Shugabar Asma’u, ta ci gaba da Jan hankalin yan Jaridun bisa kamanta yin gaskiya ayayin gudanar da ayyukansu musamman a yanzu da ake tunkarar lokacin siyasa wanda al’umma baki daya suke dogara dasu kana hakan ya zame musu wajibi su yi ayyukan da kowa zasu amfana da irin basirarsu.

Ta ce ” wannan shi ne karo na farko da ni nake Jagorantar wannan zama na liyafar da Fasto Buru ke gudanarwa a wannan waje kuma za mu yi iya bakin kokarin mu na ganin cewa mun ci gaba da taimakawa ayyukan zaman lafiya domin yana daya daga cikin kudirinmu.”

Shima da yake jawabi, tsohon shugaban kungiyar NUJ kuma wanda ya taba rike mukamin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa Kwamared Andrew Fadason ya godewa Allah da ya samu shugabar Kungiyar mace ta farko a Kaduna.

Fadason ya yi kira ga kowa da kowa da su ci gaba da yi wa kafafen yada labarai addu’a ba tare da la’akari da imaninsu ba yana mai jaddada cewa dole ne ‘yan Najeriya su makance da addini don samun ci gaba.

Leave a Reply