An gudanar da bikin Ranar Yaƙi da Ciwon Yoyon fitsari na Duniya a Jihar Kano
Daga Shafaatu Dauda Kano
Bikin ya fara daga fadar Sarkin Kano daga Nan ya wuce babban shataletale, zuwa asibitin kwararru, sai zuwa zagayen Gidan Gwamnati, sannan ya dawo fadar Sarkin na Kano.
Bikin ya samu halartar jami’an tsaro, mutane masu nakasa,da Kangiyoyi da Ma’aikatan lafiya,
Wakiliyar Neptune prime ta Zanta da shugabar Gidauniyar Tallafawa masu lalurar yoyon Fitsari VVF Aid Foundation Hajiya Hidaya Ahmad tace “Mutane da dama Suna cewa Yoyon Fitsari Auren wurine yake kawowa to yawanci dai ba haka bane duk da Shima din wani gwadabe ne da yake kawowar Amma Kuma yawanci Sunfi gamuwa da lalurar ta yoyon Fitsari wajen Karbar Haihuwa daga Ungozoma da Irin tsofaffi da Basu Cika sharudan yadda zasuyi sukarbi haihuwar ba ko kuma aka sami akasi ko tangarda Wurin karbar Haihuwar.
Taka dacewa Abubuwa da dama Suna janyowa kamar irin su hatsari,fadowa daga bishiya,da dai Sauran su.
Inda tace hanyoyin da yakamata abi don Kare Kai daga kamuwa da wannan lalura ta yoyan Fitsari kamar yadda likitoci suke bayani Shine,Karbar Haihuwa daga Kwararrun ma’aikatan lafiya da zarar Ciki ya Kai minzalin Haihuwa, aringa zuwa a sibiti domin lura da yadda jaririn yake da Kuma lafiyar Uwa.
KU KUMA KARANTA:NAFDAC ta lalata kayayyakin jabu na Naira biliyan 1.3 a Abuja
Daga Karshe Hidaya tayi Kira ga Al’umma da su Dena nuna wa masu wannan lalura Wariya,domin Suna Yawan kawo korafinsu akan Yawan tsangwama da kyama da akeyi musu sabida lalurar yoyon Fitsari lalura cee Matukar bacin rai tare da saka damuwa a zukatan masu Fama d ita, saka makon su Basa Jin Fitsari Sai dai Kawai suji zubarsa, sabanin mu da muke d lafiya da Sauran Al’umma,yakamata aringa jansu ajiki ana Kuma Tallafamusu musamman ma daga Mazajen su da Kuma makusan tansu da suke Zaune da su kamar iyaye Yan Uwa da Kuma Al’ummar gari.
Wakiliyar ta Neptune prime takuma zanta da Daya daga Cikin masu lalurar ta yoyon Fitsari Aisha Abdulhamid Inda tace Suna fuskantar matsaloli Sosai daga Abokan zamansu da Al’umma ana kyamatar su ba’a son ganin su awuri,Koda Yaro kagani ka bashi abu yaci iyayensa suna gani zasu kwace su wullar,Suce Kar yakara zuwa Inda kake,Yan uwanka da ya kamata su jaka ajiki tunda Ciwon Nan ba Kai ka dorawa kanka ba basayi Sun wareka Bama sa kaunar suji ance Kai Dan uwan sune kalilan ne ke tausaya musu.
Daga Karshe tayi Kira ga Al’umma da sudena kyamarsu suma mutanene kamar kowa Kuma ba’a haka suke adaba daga Sama Allah ya jarabcesu da wannan lalurar Kuma babu Wanda yafi karfin Jarrabawa.