An gano wajen da ake sayar da jarirai kan kuɗi N400,000 a Ogun

1
613

Hukumar ‘Yan sanda ta jihar Ogun ta cafke wasu mata biyu da take zargi da buɗe wajen sayar da jarirai a Agbado dake karamar hukumar Ifo a jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar SP Abimbola Oyeyemi, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an kama matan biyu masu suna Christiana Iyama da Margaret Ogwu, a watan Agusta bayan da suka samu bayanan sirri daga al’umar yankin.

Binkicen farko ya nuna cewa Christiana Iyama tana ɗaukar ‘yan mata ta riƙa haɗa su da maza domin su ɗauki ciki, da zarar sun haihu kuma sai ta sayar da jaririan ga masu buƙatarsu a kan kuɗi kusan naira 400,000.

Christiana Iyama ta shaida wa ‘yan sanda cewa ta sayar da jarirai uku ga wasu mata da ta samu ta wannan hanya.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya umarci da a kai matan biyu sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar domin fadaɗa bincike.

1 COMMENT

Leave a Reply