An dawo da tsohon jami’in ‘Anti-Daba’ Gwadabe don kakkaɓe ‘yan daba a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Rahotanni na tabbatar da cewa a ƙoƙarinta na magance faɗan daga a jihar Kano rundunar ‘yansandan jihar ta mayar da BM Gwadabe a matsayin O/C Anti daba.
Idan za’a iya tunawa Gwadabe ya taba zama O/C Anti daba sakamakon wani dalili yasa a dauke shi daga wurin a karshen shekara ta 2023.
Hakika a baya BM Gwadabe ya taka rawar gani wajen magance fadan daba a jihar Kano, sakamakon Salon da ya rika amfani da su wajen magance fadan, wanda hakan yasa da yawa daga cikin yan daban sun gudu wasu kuma suka hakura da harkar baki daya.
Sai dai bayan sauyawa Gwadabe wajen aiki fadan daba da kwacen wayoyi da babura ya dawo musamman a kananan hukumomin dake kwaryar birnin Kano, wanda hakan ya addabi mutane da yawa a jihar.
A baya Jaridar Neptune Prime ta rawaito cewar an kashe mutane da dama, a sanadiyyar fadan daba da kuma wadanda aka kashe saboda ana son kwatar musu wayoyi ko kuma baburansu, lamarin da ya jefa al’ummar Kano cikin rashin kwanciyar hankali.
KU KUMA KARANTA:Kwankwaso da Ganduje ku haƙura da rikicin siyasar nan haka domin ci gaban Kano – Kashim Shettima
Gabanin azumi da cikin azumin da ya gabata fadan daba ya yi kamari sosai a unguwannin Dorayi, Kofar Mata, Yakasai, Zango da sauran manyan unguwannin a Kano.
Babu shakka kokarin da kwamishinan yansanda na jihar Kano ya yi na mayar da Gwadabe Anti daba ya nuna matukar kokarinsa na ganin an kawo karshen fadan daba a fadin jihar Kano.
Yanzu abun da ya kamata shi ne rundunar yansandan kano da shugabannin harkokin tsaro a Kano har ma da gwamnatin jihar Kano su baiwa BM Gwadabe cikakken hadin kai da goyon baya don cimma manufar mayar da shi.
Wani abun burgewa shi ne yadda al’umma jihar kano su ke murna da sake baiwa Gwadabe O/C na Anti daba, saboda suna da yakinin Gwadabe zai kawo karshe fadan daba a jihar Kano.