An dakatar da Ronaldo daga buga wasa ɗaya saboda ya fusata ‘yan kallo

0
152

Daga Ibraheem El-Tafseer

An dakatar da ɗan ƙwallon Al-Nassr Cristiano Ronaldo daga buga wasa ɗaya saboda tanka wa ‘yan kallo a wasan da suka doke Al-Shabab a gasar ƙwallon Saudiyya.

Magoya bayan Al-Shabab sun yi ta ihun sunan ‘Messi’ – mutumin da ake kallo babban abokin hamayyar Ronaldo.

Al-Nassr ta samu nasara a wasan da ci uku da biyu a birnin Riyadh.

Kyaftin ɗin Portugal mai shekaru 39, ya rufe kunnensa sannan ya yi wata alama da hannu.

KU KUMA KARANTA: An dakatar da ‘yar tseren Najeriya Nwokocha daga wasanni kan amfani da haramtattun ƙwayoyi

Hukumar ƙwallon Saudiyya – SAFF ta kuma ci tarar Ronaldo ɗin Riyal dubu 30.

Kwamitin ɗa’a na ƙwallon Saudiyyar ya ce Ronaldo ba zai iya ɗaukaka ƙara ba.

Ronaldo ya koma Al-Nassr ne daga Manchester United a watan Disamban 2022 kuma bayanai sun ce ya fi kowanne ɗan ƙwallo karɓar albashi.

Ya zura ƙwallo 20 a cikin wasa 22 a kakar bana kuma Al-Nassr ce ta biyu a kan teburin gasar inda Al-Hilal ke kan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here