An cafke matashin da ke ‘sace’ kayayyakin masallatai a Jigawa

0
252

Rundunar ‘yan sandan Jigawa ta tabbatar wa BBC Hausa cewa an kama Abba Haruna mai shekara 21 bayan ya je ya lalata wani masallaci tare da kwashe rufin kwanonsa a ƙauyen Kanoke na Ƙaramar Hukumar Kiyawa.

Yadda masallatan ke zama bayan ya sace kayan

Bayanai sun nuna cewa ana tuhumar matashin da laifin sace kayayyaki a masallatai kusan 14 a ƙananan hukumomin Taura da Kiyawa da Jahun, duka a Jihar Jigawa

A ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni wata kotun majistare a Jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya za ta ci gaba da sauraron ƙarar wani matashi da aka zarga da bin masallatai yana sace kayayyakinsu.

Daya daga cikin masallatan da yayima aiki

Mai magana da yawun kotunan majistare na Jigawa, Abbas Rufai Wangara, ya ce ana tuhumar matashin da laifin lalatawa da kuma sace wasu kayayyaki na masallacin.

Wakilin mai unguwar Kanoke, Ussaini Wanzam Ilyasu, ya ce mako biyu da suka gabata ne matashin ya je garin nasu, inda ya ce wata ƙungiya daga ƙasar Larabawa za ta gina musu sabon masallaci, saboda haka za a rushe tsohon.

“Bayan an rushe wani ɓangare na masallacin sai ya ce ciko za a yi da shi, sannan ya zuba ƙofofi da tagogi da kwano da famfon tuƙa-tuƙa a mota suka tafi da su,” a cewar wakilin mai unguwa.

Danna wannan alamar don ganin cikakken bidiyon:

https://youtu.be/Kxf8nOOk5C0

Ya ƙara da cewa matashin ne da kansa ya biya ma’aikatan da suka yi aikin rushe masallacin. “Masu cire kwano aka ba su 5,000, su ma masu cire wayarin aka ba su 2,000. Masu bige haraba ma an ba su 5,000.”

Ussaini Wanzam ya ce tun bayan da matashin ya kwashi kayan ba su sake jin ɗuriyarsa ba, kuma lambar wayarsa ma ba ta shiga.

Mazauna yankin sun ce dubunsa ta cika ne yayin da suke jiran a zo a gina musu masallacinsu da aka rushe, kwatsam sai suka ji labarin an rushe wani a maƙwabta.

“Bayan ya je garin Katika zai cire, da ma suna da labarin na garinmu, sai suka zo wajenmu a babura suka faɗa mana sun kama wani mutum zai cire musu rufin masallaci.

“Ina zuwa wajen kuwa na ga shi ne.” Wakilin mai unguwa ya ce da aka tambayi mutumin game da kayan sai ya ce tuni har ya sayar da su.

Yanzu haka indai aka yi ruwa sai dai mazauna Kanoke su yi sallah a gidajensu, a cewar Ussaini Wanzam.

Leave a Reply