An cafke mahauta biyu bisa zargin sayar da nama mai guba a Jihar Kogi

0
265

Hukumar tsaro ta Cibil Defence reshen jihar Kogi, ta kama wasu mahauta biyu saboda zargin su da sayar da naman sa mai ɗauke da guba ga jama’a a jihar.

Mahuatan biyu da ke zaune a yankin Felele a Lokoja babban birnin jihar, sune Omachi Yakubu ɗan shekara 26 da kuma Salisu Abalaka, mai shekara 32.

Kwamandan hukumar ta NSCDC a jihar, John Kayode Oyinloye, ya bayyana cewa wasu likitocin dabbobi ne suka gano naman mai dauke da guba a mahautar Felele, daga nan suka sanar da hukumar, inda ita kuma ta cafke mahautan da ake zargi.

Hukumomin jihar sun ce ana kyautata zaton cewa mahautan sun dauko namar sa ɗin ne daga wani wuri sannan suka kawo shi mahautar ta Felele don sayarwa mutane.

Waɗanda ake zargin dai sun amsa laifin su da cewa basu san namar na dauke da guba ba, inda suka roki a sassauta musu.

Leave a Reply