An buɗe babbar kasuwar Singa a Kano bayan kammala aikin tsaftace magudanar ruwa

0
114
An buɗe babbar kasuwar Singa a Kano bayan kammala aikin tsaftace magudanar ruwa

An buɗe babbar kasuwar Singa a Kano bayan kammala aikin tsaftace magudanar ruwa

Daga Jameel Lawan Yakasai

An kammala aikin yashewa da gyaran magudanan ruwa a kasuwar Singa da ke cikin birnin Kano, wanda aka gudanar cikin hadin kai da kuma tsari a ranar Lahadi, 15 ga Yuni, 2025.

Wannan na cikin wata sanarwa da Nura Hassan Bature, mai taimaka wa shugabancin ‘yan kasuwar Singa a fannin kafafen yada labarai, ya fitar.

KU KUMA KARANTA: Gobara ta ƙone shaguna 47 a kasuwar waya ta a Kano

Sanarwar ta bayyana cewa aikin da ya fara tun karfe 7 na safe har zuwa 7 na yamma, ya kasance aikin gayya da ya hada shugabanni, ‘yan kasuwa, jami’an tsaro da ma’aikatan tsabtace muhalli, domin tabbatar da kare lafiyar jama’a da hana aukuwar ambaliya.

Kungiyar ta nuna godiya ga duk masu ruwa da tsaki da suka bayar da gudummawarsu, tare da fatan wannan aiki zai zama wata hanya ta farfado da shirye-shiryen tsaftace kasuwa da ci gaban tattalin arziki gaba daya.

Leave a Reply