An bayar da umarnin tura manyan ‘yan sanda faɗin Najeriya don ƙarfafa sashen leƙen asiri

0
147

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce za ta tura manyan jami’anta faɗin ƙasar domin inganta fannin leƙen asirinta da nufin magance matsalar rashin tsaro.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinta Olumuyiwa Adejobi ya fitar ranar Talata da maraice.

Sanarwar ta ambato Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya Olukayode Adeolu Egbetokun yana bayar da umarnin tura ‘yan sanda 54 masu muƙaman Mataimakan Kwamishinonin ‘yan sanda “domin su jagoranci sassan leƙen asiri na yankuna da jihohi da ke faɗin ƙasar.”

Ya ɗauki matakin ne bisa “burinsa” na “ƙarfafa sassan leƙen asiri na rundunar a kowane mataki da ke faɗin ƙasar a matsayin wata hanya ta shawo kan matsalar aikata laifuka,” in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: Ƴan sanda a Bauchi sun bankaɗo bindigogin AK-47 da miliyan 4.5 a maɓoyar masu garkuwa da mutane

Hakan na faruwa ne a yayin da ƙasar ke ci gaba da fama da matsalolin tsaro musamman garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna, har ma da Abuja.

Ko a makon jiya mutane sun gudanar da zanga-zanga a Abuja domin matsa lamba kan gwamnati da jami’an tsaro su dauki matakin gaggawa kan sace-sacen jama’a da ke addabar babban birnin ƙasar.

Wani sabon rahoto da kamfanin tsaro mai zaman kansa na Beacon Consulting a Najeriya ya fitar ya ce mutum 9, 734 sun rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta’addanci a faɗin ƙasar a shekarar 2023.

Ya ce an sace mutum fiye da 5,000 a ƙasar a shekarar 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here