An ƙona mutum biyu ƙurmus a Legas kan zargin sata a wurin mai POS

0
686

Rahotanni daga Legas na cewa wasu fusatattun jama’a sun kashe wasu mutum biyu da ake zarginsu da yin sata a wurin mai POS.

Mai magana da yawun ƴan sanda reshen Jihar Legas SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce lamarin ya faru ne a Unguwar Igando inda fusatattun jama’ar da ke wurin suka yi dirar mikiya kan waɗanda ake zargin inda suka ƙona su ƙurmus.

Ko da ƴan sanda suka isa wurin, jama’ar da suka yi wannan aika-aika sun watse.

SP Hundeyin ya bayyana cewa tuni aka soma gudanar da bincike.

Leave a Reply