An ƙaddamar da littattafai 50 da TETFund ta ɗauki nauyin bugawa a Hediƙwatarta dake Abuja
Daga Idris Umar, Zariya
Ministan Ilimi na Tarayyar Najeriya, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya jagoranci bikin kaddamar da littattafai hamsin (50) da Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund) ya dauki nauyinsu. Bikin ya gudana ne a hedikwatar hukumar da ke Abuja, inda aka gudanar da taron gabatar da littattafan ga jama’a.
Wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnati na bunkasa ilimi da karfafa binciken kimiyya a fannin ilimi a manyan makarantu. A yayin kaddamarwar, Ministan Ilimi ya jaddada cewa wadannan littattafai za su taimaka wajen habaka ilimi, musamman a jami’o’i, kwalejojin ilimi, da sauran makarantu a fadin kasar.
KU KUMA KARANTA:Tinubu ya rattaba hannu kan dokar bai wa ɗalibai rancen kuɗin karatu
Ya kara da cewa shirin samar da littattafai irin wannan yana daga cikin hanyoyin da gwamnati ke amfani da su domin magance matsalolin karancin littattafai a bangaren ilimi, tare da tabbatar da cewa dalibai da malamai suna da isassun Kayayyakin bincike da nazari.
Bikin kaddamarwar ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin jami’o’i, malamai, da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi. Wannan na daya daga cikin shirin da ke nuni da kokarin TETFund na inganta fannin ilimi a Najeriya.