An ƙaddamar da buɗe gadar da KMT ya gina a Rugar Fulani Potiskum (Hotuna)

0
138
An ƙaddamar da buɗe gadar da KMT ya gina a Rugar Fulani Potiskum (Hotuna)

An ƙaddamar da buɗe gadar da KMT ya gina a Rugar Fulani Potiskum (Hotuna)

Daga Ibraheem El-Tafseer

A safiyar yau juma’a ne ɗaruruwan al’ummar unguwar Rugar Fulani da ke garin Potiskum suka taru domin ƙaddamar da sabuwar gadar da Kashim Musa Tumsa (KMT) ya gina a unguwar don samar wa al’umma hanyar wucewa.

Da yake jawabi a wajen, shugaban gudanar da aikin gina gadar, Malam Hassan B Joɗa ya fara ne da godewa Allah da aka kammala aikin gina gadar lafiya. Sannan ya bayyana cewa shi wanda ya ɗauki nauyin gina wannan gada, wato Alhaji Kashim Musa Tumsa (KMT) tun can daman mutum ne mai son hidimtawa al’umma. Ya ce fiye da shekaru 20 yana irin wannan aikin.

Joda ya ce “A social media Dakta Hassan Gimba ya nuna masa yadda al’umma suke wucewa akan gadar Katako da Itace a wannan unguwar ta Rugar Fulani. Sannan aka bayyana masa cewa akwai makaranta a unguwar, wadda wannan gadar ta kanta yara ɗalibai suke wucewa su je makarantar. Amma duk lokacin da ruwan sama ya zo sai ya tafi da gadar Katakon, shi ke nan ɗalibai ba za su je makaranta ba.

KU KUMA KARANTA: Taron KMT-BOND ta tallafawa masu ƙaramin ƙarfi a jihar Yobe

Sannan akwai waɗanda suka rasa rayukansu ta dalilin karyewar wannan gadar Katakon. ‘Yan siyasa da dama sun yi alƙawarin gina musu gada ɗin amma sun gagara yi. To sai Allah ya kawo KMT, kuma cikin mako uku an kammala aikin.” Inji shi

KMT ya duba yara ɗaliban makaranta da suke wucewa kuma ga ɗimbim al’umma da bin wannan gada a kullum, shi ya sa ya gina gadar, don sauƙaƙawa al’umma. Gadar ita ce ta haɗa unguwar Rugar Fulani da Unguwar Dubai (bayan GGSTC Potiskum).

Ɗalibar makarantar ce ta buɗe gadar tare da mai unguwar yankin da Malam Hassan Joɗa. Jama’ar unguwar suna ta murna da fatan alheri ga KMT.

Mai unguwar yankin Malam Saleh Garba ya yi godiya da nuna farin ciki da wannan aiki. Ya ce a da ana ƙira na da mai unguwar gadar Katako, amma daga yanzu na san sunan zai koma mai unguwar gadar KMT.

Maza da mata da matasa ne suka yi cincirindo a wajen buɗewar, suna ta murna da farin ciki.

Leave a Reply