Amfanin kokumba a jikin ɗan Adam

3
824

Amfanin cin ɗanyan gurji ko kokumba suna da yawa kamar yadda wani masanin ilimin haɗa magunguna mai suna Gurama Gurama A. ya bayyana.

Cucumber na daga cikin dangin kayan marmari daga cikin rukunin Cucurbitaceae, kuma tana ƙunshe da ruwa mai tarin yawa.

Gurama yace cucumber na taimakawa wajen rage rashin ruwa a jiki ballantana a lokutan zafi. “Mutane na cin cucumber ne a matsayin kayan lambu amma tana cikin kayan marmari.

Ana amfani da ita a cikin wasu kayayyakin gyaran fata. Kayan marmari ce kamar kankana da kabewa.” In ji shi. Tana kunshe da sinadaran Vitamin irinsu A, B, C, K, potassium da Manganese waɗanda ke da matukar amfani a jikin dan Adam.

Ga wasu daga cikin amfanin cucumber kamar yadda Gurama ya bayyana:

1. Tana taimakawa wajen narkewar abinci.

KU KUMA KARANTA: Amfanin Habbatatussauda ga ɗan adam

2. Tana taimakawa wajen rage ƙiba.

3. Tana taimakawa wajen ƙarin lafiyar kwakwalwa.

4. Gurji na warware gajiyar jiki.

5. Gurji na ƙunshe da sinadaran vitamin B1, B5 da B7.

6. Tana hana warin baki da fitar numfashi.

7. Gurji na hana ciwon ƙoda.

8. Gurji na maganin ciwon ido.

9. Gurji na taimakwa wajen daidaituwar ƙarfin bugawar jini daga zuciya.

10. Akwai yiwuwar gurji ta kare mutum daga cutar sankara.

3 COMMENTS

Leave a Reply