Amfanin Habbatatussauda ga ɗan adam

3
1152

Mujalla ta kawo mana binciken zamani kan magungunan da Habbatus-sauda ke yi ga jikinmu. Mu na fata Allah Ya sa mu dace, amin.

Ana kiran Habbatus-sauda da sunaye da yawa, misali ana kiranta da”Habbatul Baraka” da larabci, wato ƙwaya mai albarka. Da turanci kuma ana kiran ta da ‘the blessed seed’, Black Cumin, Nigella Sativa, Black Caraway da sauransu.

Binciken ya danganta habbatus-sauda da matuƙar amfani wajen magance cututtuka daban-daban, sannan ta na taka muhimmiyar rawa wajen kiwon lafiya, cikin yardar Mai Duka.

Ana samun Habbatus-sauda daga ‘ya’yan tsiron “Nigella sativa”.  Hakanan an gano cewa, Shekaru aru-aru da suka gabata dubun-dubatar al’ummar nahiyar Asia da Afirka ke amfani da ita a fannin kiwon lafiya da kuma magance  wasu cututtuka dake addabar jikin dan-adam.

Ba tare da ɓata lokaci ba, ga jerin magunguna 31 da ake samu daga  wannnan tsiro mai albarka, da fatan za’a jarraba domin ganewa ido amfaninta.

ƙwayar habbatus sauda, tareda man habbatus sauda

1.  Matsalar Tsakuwar ƙoda/Mafitsara;  Ana amfani da Habbatus Sauda domin fitar da tsakuwar ƙoda ko ta mafitsara. Yadda za a haɗa wannan maganin shine, a samu habbatus sauda mai kyau, da kuma zuma marar haɗi, sai a cakuɗa su sannan a zuba ruwan zafi a rinka sha. Da yardar Allah za a samu waraka.

Hakanan za a iya amfani da wannan haɗin don kawar da matsalar fitsari musamman ga maza tsofaffi dake fama da wannan matsala.

2.  Maganin Ciwon Kai; An tabbatar da cewa, ta na magance ciwon kai. Domin samun wannan fa’ida sai a haɗa garin habbatus-sauda da ruwan Kal, ake sha sannan kuma a dinga ɗigawa a hanci don samun afuwa daga matsanancin ciwon kai.

3.  Samar da isasshen ruwan nono ga mace mai shayarwa; Wani lokacin akan samu mace ta haihu amma kuma ta rasa isasshen ruwan nonon da za ta shayar da jaririnta, idan  har haka ta kasance, sai a samu garin habbatus-sauda a hada ta da madara, mace mai shayarwar ta rinka sha, idan Allah Ya yarda za ta samu isasshen ruwan nonon da za ta shayar da jaririnta.

4.  Maganin Tsutsar Ciki; Habbatus-sauda na maganin tsutsar ciki. Ga duk mai fama da wannan matsala sai ya samu garin habbattus sauda ya gauraya ta cikin ruwan kal ya ke sha.

5.  Ƙara ƙarfin garkuwar jiki; Wani bincike da wasu masana su ka gudanar kan habbatus-sauda ya tabbatar da cewa, yawan amfani da ita na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarawa garkuwar jikin dan adam karfi.

6. Rigakafin kamuwa daga cututtuka; Wani bincike ya gano cewa, yawan amfani da Habbattus-sauda wata hanya ce ta magance duk wata cuta da ka iya yiwa jikin ɗan Adam barazana. Ta na yin wannan aiki ne ta hanyar samar wa da jikinmu garkuwa mai ƙarfi ta yadda cutukan da kan kai wa jiki hari ba za su iya tasiri gare shi ba.

7.  Daƙile yaduwar kwayoyin cutar cikin jiki; Hakanan wani bincike da aka gudanar kanta ya bayyana cewa, ta na daƙile girman ƙwayoyin cuta a jikin mutum, baya ga haka ta na hana yaɗuwar kwayoyin cutar ga sassan jikinmu.

8.  Idan mutum na fama da yawan rashin lafiya, ya samu madara kofi ɗaya, kyakkyawar zuma marar haɗi babban cokali uku, da kuma garin habbatus-sauda babban cokali ɗaya, sai a haɗa su a cakuda su sosai, sannan ake sha kullum, Insha Allahu zai samu afuwa daga ciwon, baya ga haka kuma jikin mutum zai samu kuzari.

9.  Maganin gyambon ciki; Ga wanda ke fama da wannan larura sai ya samu garin hulba , da garin habbatus-sauda , da zuma, ya hada su waje guda ya gauraya su , sannnan ya dinga sha da safe, kafin ya ci komai, kuma idan ya sha kar ya karya sai bayan awa daya. Haka zai yi da rana, da dare. Hakanan idan ya so zai iya samun man hulba ya dinga sha da zuma. In sha Allahu zai  sami waraka.

10.  Maganin asma; don samun wannan fa’ida sai a zuba man habbattus-sauda ɗigo 5 zuwa 15 (gwargwadon shekarun wanda zai amfani da ita), a cikin shayi ko tafashashen ruwa a ke sha.

  1. Ciwon Kunne; Ana amfani da habbatus-sauda wajen magance ciwon kunne. Abubuwan da mutum zai tanada sune, ƙwayar habbatus-sauda, man habbatus-sauda da kuma man zaitun.

Yadda za ka haɗa shine, tun da farko za ka soya ƙwayar habbatus-sauda sama-sama sannan sai ka nike ta don ka sami garinta, sai ka haɗa da rabin cokali na man habbatus-sauda da kuma rabin cokali na man zaitun ka gauraya su da kyau. Bayan ka tabbatar sun hadu, sai ka adana wannan hadi cikin mazubinka mai tsafta wanda kuma yake da murfi gudun kar ya zube.

Yadda za kai amfani da shi kuwa shine, sai ka samu sirinji ka ke yin amfani da shi wajen ɗigawa a kunne sau biyu a rana.

  1. Maganin zubewar gashi;  Wasu matan kan fuskanci matsalar zubar gashin kansu. Ga masu fama da wannan matsala za su iya yin 
    amfani da habbatus-sauda wajen magance wannan matsala. Sai dai a nan za a yi amfani da man habbatus sauda ne ba da garinta ba. Yadda za a yi shine a samu man habbatus sauda da man zaitun ma su kyau, sai a haɗe su waje guda. Sai ki tsefe gashin ki shafe kan da wannnan hadi na man habbatus sauda da na zaitun, sai dai ya na da kyau ki tabbatar man ya samu ƙasan gashin sosai.
  2. Gayaran fata; Habbatus sauda ta shahara ƙwarai da gaske wajen gyaran fata. Tuni aka jarraba wannan haɗin mai sauki kuma aka ga fa’idarsa. Wannan hadi ba shi da wata wahala kamar yadda muka ambata a sama. Za ki samu garin habbatus sauda ki hada da man zaitun ki cakuda su waje guda, sai ki shafa wannan haɗin a fuskar ki, za ki jira har misalin awa ɗaya sannan ki wanke. Matuƙar ki ka juri yin amfani da wannan haɗin na habbatus sauda to fuskarki za ta yi sumul, sheƙi da kuma taushi.
  3. Maganin rauni ko ciwo; Domin samun wannan fa’ida ta habbatus sauda, mutum zai shafa a saman ciwon ko raunin,  da iznin Allahu( S.W.T) za’a samu waraka.
  4. Maganin ƙunar wuta; Kamar yadda ake amfani da ita wajen warkar da rauni ko ciwo haka kuma ake amfani da habbatus sauda wajen warkar da kunan wuta. Idan har tsautsayi ya faru mutum ya kone zai yi amfani da habbatus sauda kamar yadda zai yi akan rauni ko jin ciwo, wato ya shafa a saman ƙunan.

16.  Maganin matsalar Jinin al’adar Mata.

  1. Habbatus-sauda na samar da kuzarin jiki.

18.  Ana amfani da ita wajen gyaran Fata.

19.  Maganin matsanancin tari da Mura.

  1. Maganin ciwon ciki; Anan za ayi amfani da man Habbattus-sauda ne.
  2. Tana maganin ciwon shanyewar bangaren jiki.
  3. Ana sarrafa ta wajen maganin yanar ido.
  4. Maganin rage nauyin jiki ga masu kiba ko teba.
  5. Maganin ciwon zuciya.
  6. Habbattus-sauda na saukar da hawan jini.
  7. Gyaran Gashi.
  8. Kara yawan maniyyi.
  9. Magance Cutukan Fata.
  10. Man Habbatus sauda na magananin ciwon ciki.

3 COMMENTS

Leave a Reply