Alvarez na Man City na shirin chanza sheƙa zuwa Atletico Madrid

0
59
Alvarez na Man City na shirin chanza sheƙa zuwa Atletico Madrid

Alvarez na Man City na shirin chanza sheƙa zuwa Atletico Madrid

Daga Ali Sanni

Ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Man City, Julian Alvarez, ɗan asalin ƙasar Argentina na dap da chanza sheƙa zuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Atletico Madrid dake ƙasar sifaniya.

Ɗan wasan ya yanke hukuncin chanza shekar ne duba da rashin samun isasshen gurbi a ƙungiyar ta Manchester City inda ya yanke hukuncin barin ƙungiyar.

KU KUMA KARANTA: Real Madrid ta fitar da Man City daga gasar Champions League

Alvarez dai yaci kofuna da dama tare da ƙungiyar ta Manchester City, amma duk da hakan yafison chanza sheka domin samun isasshen gurbi buga wasa.

Ana sa ran cinikin tsakanin ƙungiyoyin biyu bazai ja wani dogon lokaci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here