Al’ummar Gwammaja a Kano sun shiga jimamin tunawa da rashin da sukai na faɗuwar Jirgin sama a yankin
Daga Jamilu Lawan Yakasai
A ranar 04 ga watan mayu ta 2002, wani Jirgin sama ya yi hadari a Unguwar Gwammaja da yankin karamar hukumar Dala a Kano, wanda ya kasance shekaru 23 kenan.
A ranar 4 ga Mayu, 2002, jirgin da ke aiki a hanyar, BAC One-Eleven 525FT tare da fasinjoji 69 da ma’aikatan jirgin 8, ya fada cikin unguwar Gwammaja Quarters, wani yanki mai yawan jama’a a nan jihar kano, wadda bata da nisa da filin tashi da saukar jiragen sama, na Malam Aminu Kano, wanda yayi sanadiyar mutuwar fasinjoji 66 da ma’aikatan jirgin 7.
Read also: An kashe ƙasurgumin ɗan fashin da ‘yansandan Kano ke nema, Baba Beru
Bugu da kari, adadin mutane 103 da suka mutu, haɗarin jirgin shine mafi munin hatsarin jirgin sama da ya shafi BAC One-Eleven, Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya ta danganta lamarin da kuskuren matukin jirgin.