Allah Ya yi wa mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa Yar’Adua rasuwa

0
59
Allah Ya yi wa mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa Yar’Adua rasuwa

Allah Ya yi wa mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa Yar’Adua rasuwa

Allah Ya yi wa Hajiya Dada, mahaifiyar tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Umaru Musa Yar’adua rasuwa.

Iyalan Yar’Adua sun sanar cewa Hajiya Dada ta rasu ne a daren Litinin da misalin karfe 7 na dare, tana da shekaru 102.

Sun kuma bayyana cewa za a yi jana’izar dattijuwar da misalin karfe 1.30 na ranar Talata a gidansu da ke Katsina.

KU KUMA KARANTA: Allah Ya yi wa surkar Sarkin Zazzau rasuwa

Hajiya Dada ta rasu ya bar ’ya’ya da jikoki, ciki har da Sanatan Katsina ta Tsakiya, Abdulazeez Musa Yar’adua.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here