Alan Pardew ya karbi aikin horar da Aris ta Girka

0
309

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Tsohon kociyan West Ham da Newcastle United, Alan Pardew ya karbi aikin horar da Aris mai buga babbar gasar tamaula ta Girka.

Mai shekara 61, ya amince da ƙunshin kwantiragin kaka ɗaya da aka gabatar masa, amma da cewar za a iya tsawaita masa idan ya taka rawar gani.

Pardew bai da kungiya tun bayan da ya bar CSKA Sofia, bayan da magoya bayan ƙungiyar suke yi wa ‘yan wasansu kalaman wariya da cin zarafi.

Pardew, wanda aikin ƙarshe da ya yi a Ingila shi ne da West Brom a 2018, ya maye gurbin German Burgos.

Ya karɓi aiki a lokacin da Aris ke ta shida a teburin gasar Girka, bayan cin wasa biyu daga huɗun da ta kara a bana.

Leave a Reply